Iyaye A Kula: An kame malamar makaranta da take sakawa dalibarta yatsa a gabanta


Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta kama wata malamar makaranta 'yar shekara 32 da ke saka wa dalibarta ‘yar shekara 4 yatsa a gabanta.


Hassan Dala wanda shine mahaifin yarinyar ya bayyana cewa a ranar 11 ga Maris ‘yarsa ta dawo daga makaranta tana kukan cewa gabanta na yi mata ciwo kuma duk lokacin da za ta yi fitsari ta kan ji zafi.


Da farko na yi tunanin cewa matsalar rashin shan ruwa ne da yarinyar ba ta yi hakan yasa na gargadi mahaifiyarta ta dinga yawan bata ruwa tana sha.


Sai dai daga baya mahafiyar ta shaidamin cewa yarinyar ba ta daina kukan jin zafi ba a duk lokacin da take yin fitsari har akwai alamun jini a gabanta. 


Hakan yasa muka yi gaggawar garzayawa zuwa asibiti wanda bayan munje Likita ya sanar damu cewa yarinyar ta samu rauni a gabanta ta hanyar neman shigar ta da karfi, Cewar mahaifinta. Hakan yasa muka matsawa yarinyar kan me ya faru da ita inda ta sanar damu cewa malamar su Aunty Zahra take saka mata yatsa a gabanta sannan ta Sakata cikin hijabi tana tilasta mata ta tsotsi nononta. Hakan yasa muka sanar da shugaban makarantar abinda ke faruwa amma ya karyata hakan kuma bai bincika ba. Hakan yasa na kai kara ga ofishin 'yan sanda. 


Yan sanda sun kai kara kotu sannan kuma a wasu lokuttan da ake sauaren karar, an tsare wannan malama. 


Kungiyoyin kare hakkin yara da aka ci zarafinsu a jihar sun baiwa mahaifin wannan yarainyar tabbacin sai sun ga abinda ya ture wa buzu nadi game da wannan magana.


Shekaru biyu da suka gabata an taba samun irin hakan a Jihar Kaduna inda wata malama ta dinga yiwa wata dalibarta makamancin hakan. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post