Yadda Fashewar tukunyar gas ta kashe mutum 5 da jikkata 40 a wajen shagalin aureYan sanda a ranar Juma'a sun ba da rahoton cewa mutane biyar ne suka mutu sannan wasu fiye da 40 suka jikkata bayan fashewar wata tukunyar iskar gas din girki a wajen wani bikin aure a Indiya. 


Jami'in ƴan sanda, Anil Kayal ya ce fashewar ta faru ne a wani kauye da ke Rajasthan lokacin da bakin daurin auren ke taruwa don cin abincin biki.


Kayal ya kara da cewa fashewar ta ruguza wani ɓangare na gidan da ke gundumar Jodhpur.


A cewar binciken farko da ‘yan sanda suka yi, tukunyar iskar gas din na cikin wani dakin ajiya ne, ya zubo, ta kama wuta kuma ta fashe. Mutane hudu ne suka mutu nan take yayin da daya ya rasu a asibiti.


Kayal ya ce adadin na iya ƙaruwa yayin da wasu da dama da abin ya shafa su ka samu ƙoƙƙkone, wasu kuma yanayin da su ke ciki ya yi tsanani.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post