Idan har wanda zan aura talakane to gwara na cigaba da zama haka har na mutu banyi aure ba


Wata Matashiyar budurwa mai suna Fatima Sheka ta jawo cece-Kuce tare da tayar da hargitsi ga samari inda ta yi wata magana wacce samari basa son jin irinta. 


Matashiyar ta bayyana cewa;

"Nifa idan har talaka zan aura to gwara na mutu banyi aure ba."


Tun bayan wallafa rubutun a shafinta na Twitter sama da mutane dubu 1 ne suka bayyana ra'ayoyinsu akan kalaman Maryam, inda da yawa daga cikin masu mayar da martani suke tofin ala-wadai akan furucin da ta yi.

Fatima Sheka


Ga wasu daga cikin tsokaci da wasu suka yi a kasan rubutun kamar haka.


Fauzeeybash

Bansan me yasa mutane ke irin haka ba, amma wallahi kiji tsoron ranar da Allah zai kamaki da gatsenki.


Zinariya

Subahanallahi baby fadi alheri ko kiyi shiru 😎


Abduljalal

Wallahi kin burgeni karki yarda ki auri talaka, ki jira har sai mai kudi yazo zaki iya kai har shekara 65 kafin kiyi aure


Muhammad

Wa-iyazubillahi! To Allah ya baki mai kudi kuma ya hanaki kwanciyar hankali.


Eng.

Gaskiya Fatima bakida ilimin addini, to kudi mutum shi yake ba kanshi? Sai ki auri mai kudin, kuma ki samu ashe kashin tsiya ne dashi sai kun yi auren ku talauce sai yaya Kenan?


Wannan kadan Kenan daga cikin ra'ayoyin da mutane suke ta bayyanawa a kasan rubutun da Fatima Sheka ta yi. Shin ku menene naku ra'ayin?


Muna dakon jin ra'ayoyin ku. 

Related
Previous article
Next article

Ads Tengah Artikel 1

Ads Tengah Artikel 2