Yadda Wasu Dattijai uku suka yiwa bebiya 'yar Shekaru 13 Fyade har suka shafa mata cuta


Ana zargin wasu mutane uku da yiwa wata matashiyar yarinya kurma 'yar shekara 13 fyade a gidan wani biredi dake a unguwar Tudun Wada ta Zariya. 


Dattijan dai sun dauki lokaci suna yiwa yarinyar fyade har sai da mahaifiyarta ta fara ganin wasu alamu na canji a tattare da ita, inda gabanta ke yawan yi Mata kaikayi. 


Mai unguwar Gangaren Kwadi Malam Mohammed Danliti ya tabbatarwa da Jaridar Aminiya faruwar lamarin inda yace bayan da mahaifiyarta ta gano canji a gabanta na yi mata ciwo ba ta yi tunanin cewa wasu ne suka aikata mata hakan ba. 


Sai daga baya daya daga cikin kawayen Kurmar ta sanarwa da mahaifiyarta cewa tana ganin bebiyar tana yawan zuwa gidan biredin ana bata kudi. 


Daga bisani ne mahafiyar Kurmar ta rutsa ta a. cikin daki ta yi mata barazarnar za ta kasheta, hakan yasa kurmar ta bayyanawa mahaifiyarta abinda ke faruwa inda ta sanar da mahaifiyarta yadda dattijan suka dinga yi mata fyade. 


Jaridar Aminiya ta yi bincike zuwa asibitin Hajiya Gambo Sawaba inda aka kai yarinyar domin duba lafiyarta, wanda likitoci suka tabbatar da anyiwa yarinyar fyade Kuma har sun saka mata cuta. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post