Dalilan Da Yasa Auren Bazawara Yafi Auren Budurwa - Bincike


Nasan wasu da yawa za su yi mamakin jin batu, amma kuma dan kuka tsaya kuka karanta abubuwan dake cikin wannan rubutun za ku iya yarda dani. 


Bazawara dai itace macen da ta taba yin rayuwar aure da namiji wanda kuma daga baya aka samu rabuwa a dalilin mutuwar mijin Ko kuma kaddara daga Allah. 


Ita kuma budurwa itace macen da ba ta taba yin aure ba ba ta taba yin wata mu'amala da wani namiji ba itace ake kira da budurwa Ko Kuma 'yan mata. 


Sai dai a mafi yawancin lokaci samari ba su son auren macen da ta taba yin aure wato bazawara sun fi son auren budurwa, sai dai wani bincike ya nuna cewa auren bazawara yana da fa'idoji sosai a aurenta. 


Sai dai a wannan rubutun za mu takaita bayani akan amfanin dake tattare da auren bazawara Kamar haka;


(1) Auren Bazawara Koyi Ne Da Annabi (SAW);

Idan ka auri bazawara ka yi Koyi da fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) domin auransa na farko da yai bazawara ya aura Nana Khadija. Idan kaima ka auri bazawara ka raya sunna ne. 


(2) Kwanciyar Hankali Ne Auren Bazawara Da Ta Girmeka;

Auren macen da ta fi ka shekaru, akwai yiyuwar samun ingantacciyar rayuwar aure matukar akwai soyayya. Domin za kallon samu kulawa sosai daga wajen ta. 


(3) Bazawara Akwai Ilimin Sanin Zaman Aure;

Hakika bazawara ta fi budurwa sanin makaman aiki a zamantakewar aure musamman ma idan ta samu saurayi wato wanda ta girma. Shiyasa za ka samu zawarawa a yanzu suna yin wuff da matasa. 


(4) Hakuri Da Iya Zama Da Miji;

Bazawara tana hakurin zamantakewa fiye da budurwa domin ita budurwa ta kware wajen yaudara. Ita kuma bazawara ta Koyi wani darasi na rashin miji ke haifarwa. 


(5) Biyayya Da Girmama Iyayen Mijinsu;

Bazawara idan ta sake yin aure a Karo na biyu za ka samu duk wani Kuskure da ta yi a baya za ta gyara, domin za ka same su da ladabi ga Mijinsu tare da girmama iyayen miji da yadda ake zama da su sabanin budurwa.


(6) Saukin Kashe Kudin Aure;

Auren bazawara ba kamar auren budurwa bane domin shi ba'a kashe kudi sosai idan aka danganta shi da auren budurwa. Samarin da ba su yi aure ba Kuma suke son su yi amma ba su da isassun kudi za su iya neman auren bazawara. 


Wannan sune kadan daga cikin faidojin auren bazawara da yafi auren budurwa tasiri Kamar yadda wani binciken masu ilimi suka wallafa. Sai dai kuma sun ce ana iya samun budurwa wacce ba ta taba yin auren ba da duk irin wannan halaye masu kyau. 


Kuma wannan ba yana nuna cewa karku auri budurwa ba, kawai dai ana so a nuna muhimmancin dake cikin auren bazawara, duk da ana samun da yawa daga cikinsu da aurensu tashin hankali ne saboda irin halayyar su. Allah yasa mudace amen. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post