Sojoji Sun Kashe Manyan Shugabannin 'Yan Bindiga


Tawagar sojin Najeriya sun kai wani farmaki inda suka yi nasarar kashe wasu manyan Shugabannin yan ta’adda su biyu a ranar Talata. 


Wadanda aka kashe sune Halilu Sububu da Gwaska Dankarami. Hakan dai na biyo bayan fitar da sunayen jerin yan ta’adda 19 da ake neman su ruwa a jallo. 


Aminiya ta rawaito cewa a ranar Litinin da ta gabata ce Babban Ofishin Tsaro ya fitar da sunayen kwamandojin ’yan ta’addar guda 19 da suka fitini duk yankunan Arewa, tare da sanya tukwicin naira miliyan biyar kan kowane daya daga cikinsu ga duk wanda ya bayar da muhimman bayanan da za su kai ga cafke su.


Jerin sunayen ’yan bindigar da Babban Ofishin Tsaron ya fitar ta bakin Daraktan Sashen Yada Labarai, Manjo-Janar Jimmy Akpor, sun hada da: Sani Dangote da Bello Turji Gudda da Leko da Dogo Nahali da Halilu Sububu da Nagona da Nasanda da Isiya Kwashen Garwa da Ali Kachalla (Ali Kawaje) da kuma Abu Radde.


Sauran su ne; Dan-da da Sani Gurgu da Umaru Dan Najeriya da Nagala da Alhaji Ado Aliero da Monore da Gwaska Dankarami da Baleri, sai kuma Mamudu Tainange.


Sai dai wasu rahotanni sun tabbatar da cewa, rundunar Operation Hadarin Daji a ranar Talata ta kawar da biyu daga cikinsu daga doron kasa, a yayin da take ci gaba da yi wa sansanoninsu barin wuta ba dare ba rana.


Daya daga cikin majiyar ta bayyana cewa, sojojin sun yi luguden wuta ta sama da kasa kan maboyar Alhaji Ganai da ke Dajin Kidandan a Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.


Majiyar ta ce daga bayanan da suka samu an kashe Halilu Sububu da Gwaska Dankarami da kuma da dama daga cikin mayakansu.


A cewarta, mayakan nasu da aka kashe sun hada da; Ceri, Dan Musulmi, Danbarkeji, Guguwa, Dan Sha Bakwai, Marshall da kuma Hana Zuwa.


“Sakamakon hare-haren da aka kai wa gidan Alhaji Ganai, an kashe ’yan ta’adda da dama ciki har da Yellow Kano, wani na hannun daman jagoran ’yan ta’addan da kuma karin wasu masu tayar da kayar baya bakwai,” a cewar daga cikin majiyoyin.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post