Yadda wani Saurayi Ya Kashe Kansa Kan Zargin Satar Kudi N40,000 A Adamawa


Wani matashi mai shekara 34 ya kashe kansa ta hanyar rataya bayan da aka zarge shi da satar kudi N40,000 tun kimanin watanni 8 da suka wuce. 


Bayanai sun ce marigayin wanda ke zaune a yankin Kwanan Waya a Karamar Hukumar Yola ta Kudu a Jihar Adamawa, ya rataye kansa ne a jikin wata bishiya.


Shafin Aminiya ta tattaro cewar an tuhumi matashin wanda magini ne da laifin satar kudin dan uwansa a watan Afrilun 2022.


Tun bayan wannan zargi da aka yi wa matashin ya jefa shi cikin kuncin rayuwa, lamarin da ake zargi ya sa ya yanke hukuncin aikata wannan danyen aiki.


An tsinci gawarsa a rataye kwanaki biyu bayan mutuwarsa a Karamar Hukumar Girei, inda yake aiki, lamarin da ya jefa al’umma cikin rudani.


Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa rundunar tana gudanar da bincike a kan lamarin. Ya gargadi jama’a da su guji daukar doka a hannunsu.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post