Yadda sojin Najeriya suka yi luguden wuta a maboyar yan ta’adda a Kaduna


Rundunar sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe yan bindiga a maboyar su dake dazukan Kaduna tare da kwato makamai masu yawa a yayin kai harin. 


Anyi nasarar kashe mayakan ne a wani sumame da dakarun soji suka kai musu a maboyarsu inda aka dinga yi musu lugudan wuta ta jiragen saman yaki. 


A hirar da yai da BBC Mr Samuel Aruwan ya ce an kai farmakin ne a maboyar yan bindigar dake Chikun, Igabi, Kajuru da Giwa. Wanda a yayin kai harin an Kashe yan bindigar da dama tare da kwace makamansu. 


Kawo yanzu dai babu wata sanarwa na adadin yan bindigar da aka kashe da adadin makaman da aka kwato, sai dai an yi nasarar kubutar da mutane da dama da aka yi garkuwa dasu. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post