HOTUNA: Ɗankwambo na shirin Kwana Casa'in ya aurar da ‘yar sa ta uku, Murshida


Jarumin barkwanci a finafinan Kannywood Nura Yakubu wanda ake kira da Ɗandolo Ko kuma Yaya Ɗankwanbo a cikin shirin nan mai dogon zango na kwana Casa'in.


Shafin Film Magazine ya rawaito cewa a ranar Lahadi 20,11,2022 aka daura auren Murshida Nura Yakubu da angonta Yakubu Muhammad Lawal Maiharawa a masallacin filin kashu na unguwa Uku cikin birnin Kano kan sadaki dubu 40.


Dayawa daga cikin ƴan film musamman na shirin Kwana Casa'in sun halarci bikin, irin su Umma Shehu, Hauwa Ayawa, Falalu A Dorayi, Nazir Adam Salihi da sauransu. wanda Ɗankwambo ya nuna jindadinsa da godiyarsa.


Wannan ce dai ƴarsa ta uku da ya aurar, kuma yana cike da farin ciki sosai yadda aka yi biki lafiya aka gama lafiya kowa yana murna.
Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post