Akwai yuwuwar a yanke wa Mawaki 442 shekaru 6 a gidan yarin kasar Nijar


Kamar yadda rahotanni su ka bayyana wanda makusanciyar mawaki Mr 442, Murja Ibrahim Kunya ta bayyana a shafinta ta TikTok, mawakin da abokinsa Ola of Kano sun je kasar Nijar inda su ka yi badda kama su ka je yin fasfotin fita kasa da kasa wato International Passport.


Sanin kowa ne cewa in har mutum ba dan kasa bane, babban laifi ne yaje yin passport a kasar da ba tashi ba. Yayin da 442 da abokinsa su ka yi aski don su samu passport din zuwa kasashen da aka haramta wa ‘yan Najeriya zuwa, ta Nijar, sai aka yi ram dasu.


Yanzu haka an sakaya su a gidan gyaran hali inda su ke jiran hukuncin da za a yanke musu. Akwai yuwuwar a yanke ko ko wannensu shekaru 6 a gidan yari.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post