Yadda Wasu matafiya suka kone kurmus a hatsarin mota a kan hanyar Abuja



A Kalla matafiya 17 suka kone kurmus a sakamakon wani hatsarin mota da ya faru a hanyar Abuja. 


Shafin Hausa na Radio Faransa ya rawaito cewa motar ta taso ne daga jihar Gombe  zuwa Lagos dake kudancin Najeriya wanda hatsarin ya faru a hanyar Abuja zuwa Lokoja a ranar Talata. 


A zantawar su da daya daga cikin mutanen da suka shaida lamarin, Kabiru Garba, ya bayyana cewa, motar kirar Toyota Hiace mai kujeru 18 ta ci karo ne da wata katuwar motar dakon kaya a kusa da marabar Yaba, akan hanyar Abuja zuwa Lokoja.


Garba ya kara da cewa, motar bus din ce ta manno a guje ta kuma ci karo da katuwar motar ta baya, lamarin da ya sa bus din ta kama da wuta nan take.


Tuni jami’an kwana-kwana suka isa wurin da hatsarin ya auku domin kashe wutar da ta tashi, yayin da a gefe guda, jami’an kiyaye hadurra na FRSC ke aikin ceto.


Hanyar Abuja zuwa Lagos ana yawan samun hatsari wanda hakan ke jawo asarar rayuka da asarar dukiyoyin al'umma. Ana danganta hakan da rashin kyaun hanya da kuma gudun wuce sa'a da direbobin suke yi. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post