Wata mata ta zubawa mijinta guba a abinci ya ci ya mutu saboda bata son ya kusance ta
Wata mata mai suna Fatima Abubakar da ake zargin ta da zubawa mijinta mai suna Goni Abba guba a cikin abinci ya ci ya mutu saboda bata son auren. 


Hukumar ƴan sanda reshen jihar Borno ta yi nasarar kame matar, wanda Kwamishina CP Abdu Umar ya bayyana haka ga hukumar dillancin labarai NAN.


Ya ce a ranar Asabar ne suka kame matar da ake zargi da kashe mijinta wanda shine limamin masallacin garin, bayan ya dawo daga Sallah sai matarsa Fatima wacce ita ce mata ta biyu ta zuba masa guba cikin abincinsa.


Abdu Umar ya ce bayan da Goni ya fara cin abincinsa sai yaji jikinsa ya canja wanda hakan yasa aka dauke shi don zuwa asibiti, sai dai kafin akai ga zuwa asibitin rai yai halinsa.


Bayan samun rahoton abinda ke faruwa muka tura jami'an mu domin kamo matar da ta aikata laifin, sai dai da jami'an suka je gidan suka iska mutanen unguwar sun cika gidan suna ƙoƙarin kashe matar.


Sai dai jami'an namu sun yi kokarin dakile yunkurin matasan, wanda hakan yasa jami'an namu suka kamo wacce ake zargin da kashe mijinta. kuma wacce ake zargin ta amsa laifinta na zubawa mijinta guba a abinci, inji CP Abdu Umar.


Sai dai a lokacin da kamfanin dillancin labarai NAN ya zanta da ita kan dalilan da yasa ta zubawa mijinta guba a abinci ya mutu, Fatima ta bayyana cewa ita ba ta san sa kuma ta gaji da zama dashi.


Goni mijina ne na biyu kafin na aure shi na taba yin aure kuma auren ya mutu saboda bana son auren daga baya kuma na kara auren wannan mijin nawa da na kashe saboda auren ya isheni, inji ta.


Domin ina yawan zuwa gidan iyaye na ina sanar musu cewa nifa banson wannan auren domin ya isheni amma kullum sai dai su ce na yi hakuri. Domin akwai wani lokaci bayan na haihu sai na bar gidan na koma wani kango da zama har tsawon sati biyu.


Ta ce mijinta babu abinda baya yi mata kuma basa yin fada kawai dai ita auren ne bata so, amma kawai na tsani duk lokacin da mijin nawa zai kusance ni, bansan abinda ke damuna na ba, cewar Fatima.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post