Jarumar Kannywood Rahama Sadau Ta Lashe Kyautar Gwarzuwar Finafinai Ta Africa

Rahama Sadau ta lashe kambu


Fitacciyar jaruma a masana'antar Kannywood Rahama Sadau ta lashe gagarumar kyauta ta gawrzuwar jarumar Afrika a wani taro da aka shiryawa na jaruman finafinai a birnin Toronto na ƙasar Canada.


Rahama Sadau ita ce ta bayyana hakan a wani rubutu da ta wallafa a shafinta na facebook a ranar Lahadi, inda ta wallafa hoton kyautar da ta samu tare da rubuta cewa itace ta lashe gwarzuwar jaruman Afrika na ɓangaren Nollywood.


Jarumar ta lashe kyautar ne a dalilin rawar da ta taka a cikin film ɗin Alamjiri wanda darakta Toka Mcbaror ya shirya shi cikin harshen Ingilishi wanda aka yi amfani da jaruman Kannywood da Nollywood.

Rahama Sadau ta lashe gawrzuwar finafinan ta Afrika
Rahama Sadau ta lashe gawrzuwar finafinan ta Afrika 

Ta ce tun lokacin da ta ji har da sunanta a matsayin wanda za su karbi kyautar ta yi murna sosai, domin fitar da sunanaka ma wani abin murna ne da kuma alfahari, sai gashi kuma na yi nasarar lashe gasar, Inji ta.


Jarumar ta bayyana godiyarta ga maigidanta AY, ɗan wasan barkwanci domin irin damar da ya bata da kuma Toka Mcbaror kan irin kokarin da yake yi a koda yaushe.


Ina taya murna ga dukkan wanda muka yi aiki dasu tare domin nasarar duka ta mu ce gabaki ɗaya. kuma ina tsumayen lokacin da Mutane za su kalli shirin film din Almajiri.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post