BINCIKE: Dalilai 5 da yasa mata ke yin soyayya da mazan da ba sa so


Kamar yawancin irin yadda mata suke karantawa a cikin litattafan Soyayya da tatsuniyoyi, inda suke cin karo da labarin sarki ko yarima ko kuma wani attajiri.


Hakan yake sa wasu mata da yawa su ji aransu suna son haduwa da irin wannan mazan koda ba za su aure su ba. Sai dai da yawa mata basa samun irin waɗannan mazajen da suke burin samu.


Dayawa daga cikin mata masu karanta tatsuniyoyin soyayya suna sakawa a ransu cewa sai sun auri irin wannan mazajen, sai dai kuma a zahiri idan ka tara mata 100 kaso 99 basa samun zabin ransu.


Akwai wasu dalilai da yasa wasu matan ke yin soyayya da mazan da basa kaunarsu a zuciyarsu kawai dai suna yi ne saboda wasu abubuwa da za mu bayyana muku wasu daga cikinsu.


1. Rashin Samun Abunda Ranki Ke So;

Mata da yawa suna yin soyayya da namijin da basa son shi a zuciyarsu, amma kawai dai suna yi ne saboda rashin samun irin namijin da ransu ke so. Hakan yasa idan wani ya nuna yana kaunar su to za su karbi soyayyar sa amma bawai don ransu yana so ba.


 2. Girma (Fargarbar Tsufa);

Dalili na biyu da ke jawo mace tai soyayya da namijin da bai kwanta mata a ranta ba shine, shekaru. Wata budurwar tun ba ta yarda ta kula saurayin da yazo wajenta da soyayya, idan ta fuskanci ba ta samu irin wanda take so ba za ta fara tunanin shekaru suna tafiya hakan zai sa ta saurari duk wanda yazo wajenta amma bawai zabin ranta ba.


3. Kwadayi Da Son Abin Duniya;

Wasu matan babban abinda ke sa su yi soyayya da namijin da basa so shine kwadayin abinda yake dashi. Idan namiji yana da kudi ko wani abu makamancin haka, idan ya nuna yana son mace koda bata son sa za ta nuna tana yi saboda zai yi mata hidima kuma ya biya mata wasu bukatun ta.


4. Son Birgewa

Akwai matan da su burinsu shine su tara samari domin kawayenta ko ƴan uwanta ko kuma ƴan unguwarsu su gani domin ace ita din mai masoya ce. Hakan yasa sai kaga duk wanda yazo ya nuna yana sonta za ta bashi dama koda kuwa ba irin wanda takeso bane.


5. Kare Kai;

Wasu matan suna soyayya da namijin da basa so don kada kawaye ko ƴan unguwa su ce ba ta da saurayi, hakan zai sa ta kula wanda ya zo ya ce yana sonta koda kuwa ba irin kalar da takeso bane don dai kada a yi mata gorin ba ta da saurayi.


Wannan sune kaɗan daga dalillai da muka tattaro da yasa mata da yawa ke yin soyayya da mazan da basa kauna. Da fatan za'a amfana, kuma da fatan mata za su rage buri domin ba lallai sai kin samu wanda kike mafarki ba, ki samu wanda yake kaunarki tsakani da Allah ki aure shi. Allah ya haɗa kowa da rabonsa amin.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post