Dubun Wani Matashi Ya Cika Bayan Garkuwa Da Kansa Ya Karɓi Naira Miliyan 1 Daga Mahaifinsa


'Yan sanda a Jihar Adamawa sun kame wani matashi dan shekara 19 da zarginsa da yin garkuwa da kansa sannan ya karbi kudin fansa daga wajen mahaifinsa Naira Miliyan 1.


Matashin mai suna Emmanuel ya hada baki da wasu abokansa su uku a ranar Asabar inda suka shirya garkuwar karya Wanda daga baya suka Kira mahaifin Emanuel cewa sun yi garkuwa da dansa Kuma sai ya biya miliyan 1 za su sake shi. 


Sai dai bayan karbar kudin rundunar 'yan sanda ta zurfafa bincike inda ta kamo wadanda ake zargi Emanuel da abokansa uku da shirya garkuwar karya tare da karbar kudi har miliyan daya. 


Zuwa yanzu an kame mutum uku ana neman na hudu mai suna Abdulhamid Mohammed. Wanda Idan aka kamo musu za'a gurfanar dasu a gaban kotu domin daukar mataki akansu. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post