Tarihin Mawaki Sadiq SalehSadiq Saleh dan asalin jihar Borno ne, kuma a can ya taso yai makaranta tun daga Firamare, Sakandire har zuwa matakin jami'a.


Sadiq tun yana yaro yake da sha'awar yin waka, tun yana fita shi da abokanan sa suna ganin yadda mawaka suke yin waka sai shima sha'awar yin wakokin ya shiga ransa.


Da haka ya fara zuwa wajen da ake buga waka (studio) domin gwada basirarsa wanda kuma cikin ikon Allah ya fara gwadawa cikin Sa'a.

Sadiq Saleh


Kawo yanzu dai Sadiq ya yi wakoki masu yawan gaske wanda shi kansa yace bai san adadin su ba. Domin ya yi waƙoƙin aure, waƙoƙin soyayya da waƙoƙin siyasa wanda bai san yawan su ba.


Sadiq Saleh ya bayyana Wakarsa ta "Abin Ya Motsa Yana Dukan Rai Ya Bakin Ganga Soyayya Ce", a matsayin wakar da yafi so domin itace wakar da mutane suka san shi.


Sadiq Saleh yana rubuta wakokinsa wasu kuma baya rubutawa. Yace yana sauraran wasu mawakan musamman na ƙasashen ketare kamar Nansi Ajran, a gida kuma yafi jin waƙoƙin Usaini Danko.

Sadiq Saleh


Sadiq Saleh ya bayyana wata wakar bikin yayarsa da aka saka yai a matsayin wacce ta bashi wahala sosai. Domin itace wakar biki da ya fara yi a rayuwarsa.


Sadiq yace babban burinshi shine ya shahara yai suna a duniya ko ina a sanshi. Wanda kuma yanzu ya fara taka mataki, yana kuma addu'ar Allah zai cika masa burinsa.
Sadiq Saleh


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post