An Kame Saurayin Da Yake Yawo Ba Wando Yana Nunawa 'Yan Mata Gabansa


Wani matashi da ake zargin sa da yawo da doguwar riga idan yaga ƴan mata sai ya ɗaga rigarsa yana nuna musu gabansa domin yaja hankalin su.


Matashin ɗan asalin jihar Kano dake unguwar Na'ibawa Rimin Hamza Hisba ta yi nasarar kame shi domin gudanar da bincike akansa don gano musabbabin dalilinsa na yin hakan.


Freedom Radio Kano ta tattaro cewa matan aure na unguwar suka sanarwa da ƴan sintirin yankin Na'ibawa kan abinda matashin yake yi a yankin. 


Inda suka ce matashin yana zama a bakin bishiya da zarar ya hangi mata sun doso sai ya kwaye al'aurarsa yana nuna musu gabansa.


Da ake hira dashi matashin ya bayyanawa Freedom Radio cewa yana aikata hakan ne a duk lokacin da shiga wani hali.


Sai dai mahaifiyarsa tace ba ta san yana aikata wannan muguwar al'ada ba, inda tace za ta dauki mataki akansa.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post