Tarihin Rayuwar Maimuna Abubakar, Mome Gombe

Mome Gombe


Maimuna Abubakar wacce aka fi sani da Mome Gombe an haifeta a Jihar Gombe tayi makarantar firamare da sakandire duk a jihar Gombe wanda kuma daga baya ta koma yin rayuwa a jihar Kano.


Dalilin da yasa ake kiranta da Mome saboda asalin sunanta na Maimuna sunan kakarta ce da ta haifi babbanta wanda yasa basa iya fadar sunan shine yasa suke kiranta da Mome.


Ta Shiga masana'antar Kannywood ta hanyar wani maigidanta Usman Mu'azu wanda shima dan asalin jihar Gombe ne. Kuma suna da kyakkyawar alaka da dangin su Mome Gombe.   Kusan kowa yasanshi a family dinsu.

Mome Gombe


Wannan dalilin yasa Mome Gombe ta nuna masa sha'awarta na fara yin finafinan Hausa. Wanda hakan yasa Usman Mu'azu ya nemi izinin iyayen Mome Gombe kan su amince ta shiga sana'ar film, hakan yasa iyayenta suka amince har ta shiga sana'ar.


Mome Gombe ta fara fitowa a wani film da ake kira 'SUNANKA'. Wanda kuma daga bisani ta dinga fitowa a finfinai daban-daban. 


Baya ga harkar film jarumar tana fitowa a bidiyo na Wakoki. Hakan ba zai rasa nasaba da irin kwarewarta a fanni rawa ba. Wanda hakan yasa ta kara yin farin jini a duniya a wata waka da sukai ta 'JARUMAR MATA' da mawaki Hamisu Breaker.

Mome Gombe


Mome Gombe ta ce ba za ta taba mantawa da wannan wakar ta 'JARUMAR MATA' ba domin ta kara daukakata a duniya. Ta ce kuma har gobe tana yin alfahari da wakar.


Mome Gombe ta bayyana Sunusi Oscar 442 a matsayin daraktan da tafi jindadin yin aiki tare dashi. Sannan kuma ta ce dukkansu tana jin dadin yin mu'amala dasu.


Ta bayyana babu abinda yafi sakata farin ciki Kamar yin ibada. Ta ce duk lokacin da take ibada tana kasancewa a cikin farin ciki. 


Sai dai Mome Gombe ta ce babu abinda yafi sakata bakin ciki shine rashin mahaifiyarta. Domin duk lokacin da ta tuna tana jin babu dadi.

Mome Gombe


Tace abin farin cikin da ba za ta manta dashi ba shine ranar da mahaifiyarta ta rasu saboda irin maganganun da suka yi da irin addu'ar da ta yi mata wannan yana sa tana jin farin ciki a duk lokacin da ta tuna. 


Mome Gombe tafi saka kaya irin na al'adun Hausa irin su atamfa domin ta bayyana cewa sun fi yi mata kyau. Kuma ta ce ita kwalliya bata dame ta ba, Indai ta yi ado to aiki za ta yi. 


Babban burin jaruma Mome Gombe a yanzu shine ta yi aure, domin a shekarun baya ta taba yin aure amma ba ta haihu ba. Sai dai tana fatan idan ta kuma yin wani auren za ta samu 'ya'ya. 


Mome Gombe ta bayyana 'DANWAKE' a matsayin abincin da tafi son ci.


Mome Gombe

Mome Gombe

Mome Gombe

Mome Gombe 

Mome GombeSuleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post