Shugaban Hukumar Tace Finafinai Afakalla Zai Yi Wuff Da Jaruma Rukayya Dawayya


Shirye-shirye sun kan kama na bikin tsohuwar jarumar finafinan Hausa Rukayya Umar Dawayya da shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab'i ta jihar Kano Alhaji Ismail Na'abba Afakalla.


Duk wanda yake cikin masana'antar Kannywood yasan da wannan soyayyar ta Dawayya da Afakalla domin an dade ana yinta,  inji rahoton "Mujallar Film".


Sai dai tun da farkon fara soyayyar ba kowane yasani ba sai a yanzu ne da aski ya zo gaban goshi kowa da kowa yasani.


Mujallar Film ta bayyana cewa sun zanta da wasu daga cikin makusantan masoyan inda suka ce shirye-shirye sun riga sun gama kankama kuma an kusa yin bikin.


A baya-bayan nan dai ake ganin yadda Rukayya Dawayya take ɗora hotunan Afakalla akan status dinta na Whatsapp, Instagram, Ticktock inda take rubuta kalmomi dake nuna alamar soyayya mai ƙarfi a tsakanin su.


A baya-bayan nan ta wallafa wani hoton Afakalla a shafinta na Instagram inda ta rubuta cewa "Samin Afakalla A Matsayin Miji Abin Alfahari Ne, Ina Yiwa Allah Godiya Da Ya Amsa Addu'a Ta".


Majiyar ta ƙara da cewa akwai maganar aure a tsakaninsu, kuma duk wasu shirye-shirye sun gama kammala, daga nan zuwa Kowane lokaci za'a saka ranar da za'a yi daurin auren.


Da yawa daga cikin ‘yan fim da sauran jama’a sun taya Dawayya da Afakallah murnar wannan abin alheri da su ke shirin yi, su na faɗin Allah ya kai mu lokacin lafiya tare da addu'ar Allah ya tabbatar da alheri.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post