Raina Yana Matuƙar Baci Idan Naji Mutane Suna Cin Mutuncin Ƴan Film - Cewar Yasmin Kwana Casa'in
Fatima Isah Bala da aka fi sani da Yasmin a cikin shirin film ɗin "kwana Casa'in" da tashar Arewa 24 ke haskawa ta koka sosai akan yadda wasu mutane ke aibata ƴan film.


Yasmin jaruma ce kuma mawakiyar gambara wacce ta fito a matsayin ƴar gidan AVM Adnan a cikin shirin "kwana Casa'in".


Jarumar ta bayyana hakan ne a wata hira da ta yi da gidan "Radio Freedom Kano" inda ta ce abinda mutane suke yiwa ƴan film yake jawo wasu daga cikin jarumai basa auruwa domin ana yi musu wani kallo na daban.


Yasmin ta ce a yanzu ba ta da wani buri da ya wuce ya yi aure.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post