Sama Da Mutane 30 Suka Nutse A Cikin Ruwa Domin Tsira Daga Harin Ƴan Bindiga A Zamfara


Rahoto na nuni da cewa kusan mutane 30 ne suka nutse a wani tafki domin gujewa harin ƴan bindiga a kauyen Birnin Waje dake yankin ƙaramar hukumar Bukuyum ta jihar Zamfara.


Jaridar Aminiya ta rawaito cewa a zantawar su da wasu mazauna garin sun shaida musu cewa maharan sun shigo garin ne a daren Laraba wanda hakan yasa hankalin kowa ya tashi inda manya da yara suka fara neman tsira da rayukansu.


Hakan yasa mutanen garin suka nufi gaɓar wani kogi domin tserewa a cikin kwale-kwale, sai dai nauyin mutanen yasa kwale-kwalen ya kife dasu a cikin ruwan.


Wani da lamarin ya rutsa da shi ya bayyanawa Aminiya cewa akwai ƴaƴan ƙanwarsa su uku da suka nutse a cikin ruwan a lokacin da kwale-kwalen ya kife.


Duk da haka sai da ƴan bindiga suka nufo wajen kogin inda suka dinga harbe-harbe wanda hakan yasa direbobin kwale-kwalen suka dinga fadawa Cikin ruwan domin tsira da rayukansu.


Sai dai duk da haka wasu da dama sun tsira inda suka haura zuwa gaɓar kogin, sai dai kuma har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ba'a samu wasu daga cikin waɗanda suka nutse a kogin ba.


Wata majiya ta bayyana cewa haryanzu maharan suna cikin garin wanda hakan yasa aka kasa ceto mutanen da suka nutse a cikin Kogin.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post