MUHAWARA: Mata Sun Bayyana Wasu Abubuwa 5 Da Basa So Daga Namiji


Mai amfani da shafin sada zumunta, Thapz ya tambayi mata a Twitter su bayyana ra'ayin su akan abubuwan da ba sa so a jikin namiji, inda lamarin ya jawo martani da maganganu masu zafi a Twitter.


Kama daga dabi'u, fita ta jiki har zuwa halaye, mata sun tofa abinda ke zukatansu, inda suka bayyana ababen da ba su so game da maza.


Ga kaɗan daga cikin abubuwa da mata suka ce basu so daga namiji


Rashin tsafta, a cikin amsoshin da matan suka dinga bayarwa sun bayyana rashin tsafta a matsayin abinda suka tsana daga namiji, wasu mazan ba sa aske gashin jiki (hammata, kai, matsematsi, rashin yanke farce, mai warin baki) wanda hakan ke haifar da kazanta. 


Namiji Mai Alfahari, Matan sun kara kokawa akan irin yadda wasu mazan suke nuna fariya musamman idan suna da kuɗi ko wata daukaka da ta sha bamban da sauran maza. 


Wanda Bai Da Kuɗi, Wasu daga cikin matan sun kara da cewa basa son namiji wanda bai da kuɗi, domin ita mace tana buƙatar namiji mai kudi wanda zai riƙa bata tana gyara jikinta.


Namijin Da Bashida Kishi, matan sun koka a kan yadda wasu mazan ba su da kishin matar da suke so. Inda suka ce ba sa son irin wannan namijin.

 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

3 Comments

Previous Post Next Post