HOTUNA: Yadda Jaruman Kannywood Mata Suka Gwangwaje A Taron Tinubu A Kano


Alamu na nuni da cewa jaruman Kannywood sun karbi tafiyar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC Alhaji Bola Ahmad Tinubu. Duba da yadda Jaruman suka cashe sosai a ranar da aka gudanar da taron dan takarar a Kano. 


Bola Tinubu a ziyarar da yai a Kano inda ya bude ofishin yakin neman zabensa wanda tawagar Kannywood ke jagoranta karkashin Shugaba Abdul-Amart Maikwashewa. 


A yayin taron dai anga dandazon jaruman Kannywood wanda mafi yawancin su duk mata ne, kuma wani abu da ya Kara daukar hankali shine duk sun saka kayan Yarabawa iri daya don nunawa Tinubu goyon bayansu. 


Wannan tafiyar dai kusan za'a ce tazo da abin mamaki domin ba Kasafai aka saba ganin 'yan Kannywood da yawa sun hade kansu domin goyon bayan wani dan siyasa ba. Wani abin mamaki kuma shine yadda mata suka fito sosai don nuna goyon bayansu. 


Cikin jarumai mata da suka yi dandazo a wajen taron akwai Fati Nijar, Teema Makamashi, Mansura Isah, Safiya Adamu, Maryam CTV da sauransu. Jaruman Kannywood a kamfen din Tinubu

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post