Tarihin Rayuwar Hannatu Bashir(Hanan)

 Hanan African queen

Hannatu Bashir wacce aka fi sani da Hanan 'yar asalin jihar Kano ce anan aka haifeta a unguwar Tukuntawa. Sai dai daga baya sun bar unguwar Tukunutawa sun koma Lamido Crescent dake a yankin Nasarawa GRA inda anan ta yi karatunta na firamare da sakandire.


Hannatu Bashir ta shiga sana'ar film tun a shekarar 2012 bisa yardar iyayenta ta hanyar darakta Hassan Giggs inda ta fara fitowa a wani film na marigayi Rabilu Musa Ibro mai suna 'KOTUN IBRO'.


Tun farkon da ta fara yin film zuwa yanzu jarumar ta yi Finafinai da dama, kuma tana fitowa a matsayin budurwa, Kawa, matar aure da sauransu. Bayan haka kuma Hannatu tana shirya Finafinai. 

Hanan African queen
Hanan an African queen 


A cikin finafinan da Hannatu ta fito ta bayyana tafi son "MUTUM DA ALJAN" saboda labarin yadda aka shirya film din ya kayatar da ita. Sai dai ta bayyana fim din "KUKAN KURCIYA" a matsayin wanda ya fi bata wahala a dukkan finafinan da ta fito. 


Hanntu ta bayyana jihar Kaduna a matsayin garin da tafi son zuwa yin aiki, domin kuwa tasan mutane sosai a garin. 

Hanan African queen
Hanan an African queen 


Ta bayyana matsalar da masana'antar Kannywood ke fuskanta daga wajen Muatane gari irin yadda ake aibatasu ana zaginsu ana yi musu wani kallo daban a matsayin wanda su kansu suna bayar da gudunmuwa wajen kawo matsaloli. 


Hannatu ta bayyana mutuwar kakanta a matsayin abin bakin ciki da ba za ta manta dashi ba duba da irin shakuwa da kuma alakar dake a tsakanin su. 


Ta bayyana kasar Amurka, China da Daular Larabawa a matsayin kasashen da tafi son zuwa. Sannan ta bayyana tuwon shinkafa da miyar kubewa a matsayin abincin da tafi so. A nama kuma jaruma Hannatu Bashir tafi son naman kifi, fizza. 


Hanan an African queen 

Jaruma Hannatu Bashir ta ce nan babu dadewa za ta yi aure, ta nemi magoya bayanta kan su tayata da addu'a.

Hanan an African queen


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post