Yadda Wani Mahafi Yaiwa Yarsa Jaririya Duka Har Hannunta Ya Karye Saboda Ta Hanashi Yin Bacci


Wani mahaifi da ake zargin sa da nuna tsantsar rashin tausayi ga 'yarsa 'yar watanni biyu da haihuwa bayan da tsananin kuka da jaririyar ke yi da dare yasa yai jifa da ita kuma hannunta ya Karye wanda ya jawo aka yanke hannun jaririyar. 


Magidancin mai suna Confidence Amatobi dan kimanin shekaru 31 da haihuwa dan asalin garin Amurie ne a karamar hukumar Isu  ta jihar Imo ya karya hannun 'yarsa sakamakon damunsa da tai da kuka lokacin da yake tsaka da yin bacci. 


A dalilin hakan yasa wasu daga sassan jikin jaririyar ya Karye wanda cibiyar kula da lafiya ta tarayya (FMC) dake garin Owerri suka tabbatar da cewa sai an yanke hannun jaririyar guda daya domin ba zai gyaru ba. 


Wanda ake zargi da aikata laifin Confidence Amatobi lokacin da ya gano hannun jaririyar ya Karye ya yi yunkurin yin amfani da itace da igiya na roba don daure hannunta, cewar matarsa. 


Hakan yasa ya kulle jaririyar ita da mahaifiyarta a daki tare da karbe wayarta har tsawon kwanaki biyu don kar ta sanarwa da makota abinda ke faruwa. Wanda hakan yasa hannun jaririyar ya rube har aka kai ga yanke shi. 


Kawo yanzu dai kungiyar kare hakkin dan adam da Kungiyar mata 'yan jarida ta Najeriya NAWOJ sun yi tofin Allah tsine game da wannan aika-aikar da wannan mahaifi yaiwa 'yarsa. 


Sannan sun yi kira ga gwamnatin jihar Imo da hukumar 'yan sanda da su yi gaggawar nemo wannan mutumin da ya aikata rashin Imani ga yarsa na cin zarafi don a gurfanar dashi a gaban kotu. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post