Bankin Polaris ya gargadi ma'aikatan musulmi da su guji halartar sallar Juma'a


A wani gargaɗi da bankin ya fitar ta sakon email mai ɗauke da bayanai a ranar Talata inda suka ja hankalin ma'aikatan su Musulmai akan su daina zuwa Masallacin juma'a domin ya saɓa da dokar aikin bankin.


Damilola I. Adebara shine wanda ya fitar da sanarwar inda yace a tsarin aikin banki babu maganar ibada, kuma shi aikin banki ana yinsa ne har lokacin da za'a tashi kamar yadda dokar bankin ta tsara. Amma ba zai yiwu ba lokacin aiki a tafi wajen ibada ba.


Wannan sanarwar dai ba ta yiwa Musulmai daɗi ba duba da dukkan wani ɗan ƙasa yana da ƴancin sa na yin addini, ba zai yiwu lokacin ibada a hana mutum yaje yai bauta ba.


Kafar sadarwa ta Daily Reality ta tattauna da ɗaya daga cikin ma'aikatan bankin ta wayar tarho inda ta bayyana musu cewa ko a kwanakin baya irin hakan ya faru da daya daga cikin ma'aikata na bankin inda supervisor dinta ya hanata zuwa yin ibada.


Barista Abubakar Saleh mai sharhi a Kano ya bayyana cewa matakin da bankin suka ɗauka ya sabawa tsarin dokokin banki, domin babu wata doka da ta ce maaikaci ba zai je yai ibada a lokacin da aka saba.


Don haka abinda bankin yai ya saɓa da tsarin dokokin kasa, don haka muna kiransu da su yi gaggawar janye kalamansu kuma su baiwa musulmai hakuri kan wannan furucin nasu.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post