Caccakar Da Rarara Yaiwa Ganduje A Sabuwar Wakarsa Ta Tayar Da Hargitsi


Shahararren mawaƙin siyasa a arewacin Najeriya Dauda Abdullahi Kahutu Rarara ya caccaki tsohon maigidansa gwamna Abdullahi Umar Ganduje a wata sabuwar wakarsa.


Rarara ya bayar da gudummawa sosai a tafiyar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje tun daga farkon kafuwarta a zaɓen 2015 zuwa 2019 har zuwa cikin 2023 kafin Rarara ya fita daga Jam'iyya mai mulki ta APC zuwa ADP.


Mawaƙin dai shine shugaban tafiyar 13×13 ta Kannywood da suke goyon bayan ɗan takarar shugaban kasa Ahmad Bola Tunubu. Sai dai wani rahoto ya tabbatar da cewa Rarara baya goyon bayan tafiyar ɗan takarar gwamna da Abdullahi Umar Ganduje ya fitar.


Rarara ya bayyana goyon bayansa ga ɗan takarar gwamna a jam'iyyar Action Democratic Party ADP wato sha'aban Ibrahim sharada.


A Sabuwar wakar da Rarara ya fitar a baya-bayan nan ya yi habaice-habaice inda ya kira Ganduje da 'HANKAKA' sannan kuma a cikin wakar ya tabbatar da rikicinsa da gwamna Ganduje, sannan kuma ya kira gwamna da cewa mai fuska biyu.


A cikin wakar Rarara ya soki gwamna Ganduje da taka rawa wajen kin saka sunansa cikin kwamitin kamfen ɗin ɗan takarar shugaban kasa Bola Tunubu.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post