An Ƙara Samun Adadin Mutum 108 Da Suka Mutu A Sakamakon Ambaliyar Ruwa A Jigawa


An sake samun adadin mutane 108 da suka rasa rayukansu a sanadiyyar ambaliyar ruwan sama tun daga watan Agusta zuwa karshen watan Satumba.


RFI Hausa ta rawaito cewa, a ranar Asabar ne kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Jigawa Lawan Adamu ya tabbatar da adadin waɗanda suka rasa rayukansu a sanadiyyar rugujewar gine-gine, tsawa da kuma waɗanda ruwa ya cinye su.


Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan jihar, Muhammad Badaru ya dawo daga balaguron da ya yi zuwa kasashen waje a ranar Juma’a, bayan da ya shafe makwanni 3.


Gwamna ya sha caccaka a kan yadda ya zabi ya yi balaguro a lokacin da mutanen jiharsa ke tsakar wannan bala’in, da kuma yadda ya gaza ziyartar yankunan da ambaliyar ta shafa.


Damunar bana an samu ambaliyar ruwa sosai a sassan jihohin arewacin Najeriya wanda hakan yai sanadin mutuwar mutane da dama da kuma lalata amfanin gona na tarin kuɗi masu yawa.

Related
Previous article
Next article

Ads Atas Artikel

Ads Tengah Artikel 1

Ads Tengah Artikel 2

Ads Bawah Artikel