Gaskiyar Magana Akan Cutar Dake Damun Fati Bararoji


Wasu hotunan Fati Bararoji da suke ta yawo a kafafen sada zumunta tun daga ranar Juma'a sun jawo cece-ku-ce inda aka ga tsohuwar jarumar cikin wani yanayi ta rame sosai.


Inda mutane ke ta tofa albarkacin bakinsu suna ta yin tsegumi akan halin da jarumar take ciki yadda ta rame. Wasu na ta tambayar ko batada lafiya.


Jarumar itace dai ta wallafa hotunan a shafinta na Ticktock akan status dinta. Wanda hakan yasa hotunan suka yadu a shafukan soshiyal midiya.


Sai dai hakan yasa sashin Mujallar Film ta tuntubi Fati don sanin abinda ke faruwa da ita game da lafiyar ta. Sai dai jarumar ta ce ta yi mamaki kan yadda mutane suke yada abinda ba haka bane a soshiyal midiya.


Ta bayyana cewa ita lafiyar ta kalau babu abinda ya sameni. Kawai dai wannan satin naje garin Abuja daga can kuma na tafi Sokoto biki sannan kuma na dawo Kano ba tare da yi hutu.


Hakan yasa na samu gajiya sosai kuma idanu suka fada har na rame duk a dalilin gajiya. Na yi hotuna ba tare da na samu na huta ba, shiyasa ake ganin kamar banida lafiya. Don haka masu cewa banida lafiya su sani lafiya kalau nike.


Abin dai da na sani cikin satin nan na yi tafiya zuwa Abuja, daga nan sai na wuce Sokoto wajen taron biki, kuma ban huta ba na dawo Kano. To wannan yanayi na tafiyar ya sa ni gajiya, duk ido na su ka faɗa, kuma na zo na yi hotunan a haka, shi ya sa ake ganin kamar ba ni da lafiya ko na yi wata rashin lafiya. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post