Akalla mutane 13 ne suka rasa rayukansu a lokacin da wasu 'yan bindiga suka shiga kauyen Ruwan Jema dake karamar hukumar Bukkuyum inda suka dinga harbin kan mai uwa da wabi ana tsaka da yin sallar juma'a.
Wani da lamarin ya faru kan idonsa ya shaidawa jaridar Aminiya yadda 'yan bindigar suka kutsa kai cikin kauyen. Inda yace lokacin da suka shigo ana gudanar da sallar Juma’a ana raka'a ta karshe sai suka fara harbi.
Hakan yasa kowa ya fara guduwa domin neman tsira da ransa sai dai duka da hakan sun yi nasarar kashe mutum 13 daga cikin masallatan, sannan akwai wadanda suka samu raunin harbi.
Baya ga wadanda suka kashe a yayin sallah sai da sukayi kashe wasu tun daga farkon gari wanda daga baya muka tsinto gawarwakin su a cikin gonaki. Har zuwa yanzu ana cigaba da tsinto gawarwakin wanda suka mutu, wanda hakan yasa aka samu jinkirin yi musu jana’iza.
Kawo yanzu dai wadanda suka samu raunuka a yayin harin suna asibiti suna karbar kulawa daga jami'an lafiya.