Mutane Fiye Da 130 Suka Mutu Tare Da Asarar Dukiya Ta Kusan Tiriliyan 2 Sanadin Ambaliyar Ruwa A Jigawa


Akalla mutane 134 suka rasa rayukansu tare da asarar dukiya wacce ta kai sama da tiriliyan daya da rabi a dalilin ambaliyar ruwan sama da ake fama da ita a sassan jihar Jigawa a cewar gwamnatin jihar. 


Alhaji Umar Namadi wanda shine mataimakin gwamnan jihar ya bayyana hakan ga hukumar Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) a ranar Asabar yayin wata ganawa da yai da babban jami'in hukumar a ofishin sa. 


Namadi ya shaida musu cewa ambaliyar ta jawo tashin kauyuka da dama tare da lalata tituna sama da 20 da karya gadoji sama da 10. Yanzu kuma ambaliyar tana cigaba da mamaye sassan jihar inda ta tunkari gabashin jihar. 


Yace ambaliyar tai sanadin raba mutane da muhallin su, inda ya koka kan yadda madatsun ruwan jihar suka cika da yashi da suke bukatar a yashe su, wanda hakan na daga cikin dalilin jawo ambaliyar. 


Yace suna da kididdigar wanda ambaliyar ta shafa inda mutum 272,189, daga cikinsu 76,887 suka rasa muhallansu yayin da 134 suka rasa rayukansu. 


A karshe mataimakin gwamnan ya yi kira da gwamnatin tarayya da sauran kungiyoyin bayar da tallafi da su taimakawa jihar don kawo karshen matsalar. 


Shima a nasa bangaren jami'in na UNICEF ya yi alkawarin cewa hukumar za ta za ta taimakawa jihar da abubuwan da suka dace domin rage radadi. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post