Jam'iyyar APC Ta Dauki Jaruman Kannywood Biyar Domin Yakin Neman Zaben Bola Tinubu


Jam'iyyar APC ta saka wasu daga cikin 'yan masana'antar Kannywood cikin wanda za su yi yakin neman zaben Ahmad Bola Tinubu. Daga cikin wanda aka dauka akwai jarumai biyu da mawaka biyu da kuma shugaban hukumar tace finafinai da Dab'i ta jihar Kano. 


A ranar Juma'a ne dai aka fitar da jerin sunayen wadanda za'a yi yakin neman zaben Bola Tinubu dasu a jam'iyyar APC. Sunayen dai ya hada da manyan siyasa, mawaka, yan jarida, 'yan film na Kudu da Arewa. 


Cikin wadanda aka gayyata a kannywood akwai mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara da Jadda Garko, sai kuma jarumai wanda ya hada da Nuhu Abdullahi, Sani Idriss Kauru(Moda) sai kuma na biyar Ismail Na'abba Afakalla shugaban hukumar tace finafinai. 


Afakallahu shine mataimakin darakta na reshen Kano, shi kuma Rarara shine jami'in gudanarawa, Nuhu Abdullahi mataimakin jami'in walwala na Kano sai kuma Jadda Garko wacce aka baiwa mataimakin darakta. 


Sai dai tun bayan fitar da sanarwar wanda za su yi yakin neman zaben mutane suka fara bayyana tsokacin su, inda wasu ke ganin cewa wanda aka zaba basu cancanta ba. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post