Domin Mata: Hanyoyin Da Zaki Iya Fahimatar Saurayin ki Bai Damu Da Kuyi Aure Ba


Da akwai mazan da suke haura shekarun da ya kamata ace sun yi aure amma sai a samu ba su yi auren ba, wani bincike yai nazari akan dalilan da yasa hakan yake faruwa. 


Irin wadannan mazan dai ba wai basu da lafiya ko rashin wadata bane, kawai dai aure ne baya cikin tsarin rayuwar su. Duk da haka ana samun matan dake nacewa irin wadannan mazan duk da tunanin ko zasu aure su, amma kuma basa auren su.


Shiyasa a wannan rubutun za kuji wani bincike da aka gudanar na dalilin dake jawo wasu mazan kin yin aure. Ga wasu alamun da muddin kika samu namiji yana dasu kawai ki fitar harkarsa ba zai yi aure ba.


1: Haura Shekarunsa

Duk namijin da kika ga ya haura munzalin lokacin daya dace yayi aure kuma yana da lafiya da daman yin auren yaki yi, yana cikin irin mazan da aure baya cikin tsarinsu.

Kada ma ki bata lokacinki a wajensa ba aurenki zaiyi ba nemi wani. 


2: Yiwa Mata Gadara;

Akasarin irin wadannan matan a kullum basu cika ganin darajar mata ba. A kullum suna yiwa mace kallon rashin yarda da kuma matsala.


Irin wadannan mazan a duk lokacin da za su yi mu'amala da mace sai su rika hadawa da gadara. Ko nuna isa, basu iya rarrashin mace ba.


3: Basu Da Lokacin Yin Soyayya;

Da wuya ki gansu suna son mace sai dai idan zina zasu yi da ita. Idan mace tace tana son su nan take za su nuna mata sai dai idan zina za su yi da ita.


Don haka idan kin fahimci wanda kike son haka yake kina batawa kanki lokaci ne, kiyi gaggawar rabuwa dashi. 


4: Suna Yiwa Aure Kallon Wahala Ne;

Sunfi mai aure iya tsara yadda zai zauna da matarsa. Sunfi nunawa ma'aurata kuskurensu daga waje. Haka nan gani suke idan ba ka mallaki wasu miliyoyi ba aure ba naka bane.


5: Basu Da Sha'awar Haihuwa;

Sune za ki ga suna da kushe haihuwa da kuma yawan yara. Sune za ki ji suna tsara miki rayuwar da za su yi idan sun yi aure da mace guda da haihuwa daya.


Sunada kakale da tsarafetsafe. Duk lokacin da aka musu zancen aure za su ce lokaci ne baiyi ba.

 

Irin wadannan maza bayaga matsalar kwakwaluwa, har ila yau maza ne da suke da matukar hadari a cikin al'uma. Domin sune ake yawan samunsu da yiwa yara kanana a unguwa kwakule, Fyade, luwadi da yara da kuma lalata yara mata sabbin balaga.


Ina fatan duk mace da take tare da irin wadannan mazan za su yi kokari su kauce musu su daina mu'amala dasu domin gudun yin nadama. 


Da fatan mutane za su zurawa irin wadannan mazan idanuwa a unguwowinsu domin kada su batawa yaransu tarbiya.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post