Domin Matasa: Yadda Zaku Iya Yin Sana'ar Sayar Da Data Online Kuna Kwance A Gida



Ga duk samari wadanda suke da sha'awar fara yin sana'ar sayar da Data a yanar gizo-gizo sai ku karanta wannan rubutun a nutse, domin samun cikakken bayani akan yadda zaku fara sana'ar sayar da Data. 


Wa'danda suke sayar da "data" da wa'danda suke san su fara sayar da "data" duka ku karanta zaku amfana.


Mafi yawan mutane suna san su fara sana'ar sayar da "data" amma kuma rashin sanin hanyar da za su bi wajen farawa shine yake hanasu, wasu kuma tunanin ta yaya zasu samu masu saye a wajensu shine damuwarsu, wanda wasu kuma tsammaninsu jarin da sana'ar sayar da "data" take buƙata yafi ƙarfinsu ne.


A 'dayan ɓangaren kuma su kansu wasu daga cikin waɗanda suka fara sana'ar ta sayar da "data" sun dena sana'ar ne sakamakon rashin sanin hanyar da zasu tafiyar da ita kanta sana'ar tasu.


Duk sana'a ana samun rashin riba ne a bayyane yayin da ake neman iliminta, ana samun riba kuma a bayyane ne yayin da aka samu ilimin tafiyar da ita. Anan ina maganane akan masu amsar bashi wajen masu sayar "data", wanda hakan ya karya jarin mafi yawa daga cikin masu sana'ar sayar da "data" har sun dena sana'ar.


Mafi yawan masu sana'ar sayar da "data" sun samu kansu a cikin irin wannan yanayin na aci bashin "data" a gunsu sannan aƙi biyansu, to kaima da zaka fara zaka iya kasancewa cikin irin su, kai kuma daka fara har ka fuskanci irin wannan matsalar bara kaji mafita.


"Idan ya zamana wasu mutane da kakejin nauyinsu (kunya) sannan kuma suka ci bashinka na "data" har suka ƙi biyanka, to ba barin sana'ar za kayi saboda su ba, kaine da kanka zaka nuna masu ita fa "data" kuɗi ne ake sakawa kafin a turo ma mutun ita, to idan ka kasance baka da kuɗin ta yaya zaka iya tura ma mutun ita? Idan har ka iya gaya masu haka dole zaka zauna lafiya, sannan kuma ku gane eh dole anacin bashin mutun a ko wace irin sana'a yake yi, amma fa gangancine bayar da bashi ga sana'ar sayar da "data" ko katin waya.


Mafi kuskuren da masu sana'a da masu tunanin fara sana'a suke yi shine rashin ƙulla kyakkyawar mu'amula da al'umar. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post