Mamakon Ruwa Ya Haifar Da Ambaliya Wanda Yai Sanadin Tafiya Da Gawar Mutane Fiye Da 500 A Naija


A kalla gawar mutune 500 ruwai yai awon gaba dasu a dalilin wata ambaliyar ruwa da akai a karamar hukumar Bariga ta jihar Naija. 


BBC ta rawaito cewa ambaliyar ruwan ta shafe makabartar garin wanda tai awon gaba da gawarwakin mutane 500 tare da lalata wasu kabarurruka masu yawa. 


Alhaji Alhassan ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da yai da gidan Radio na BBC Hausa. Inda yace ambaliyar ta lalata kaburbura sama da 1500.


Sai dai daga bisani an sake binne wasu gawarwakin da aka samu guda dubu daya, amma sama da 500 ne ruwan yai awon gaba dasu, inji Alhassan. 


Yace zuwa yanzu suna neman gano gawarwaki 500 da ruwan yai awon gaba dasu, inda ya daura laifin faruwar hakan ga mutanen da suke harkar ma'adanai kusa da makabartar. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post