Addu'a Kawai Nike Bukata Daga Wajen Al'umma Domin Ina Cikin Tsananin Rashin Lafiya - Cewar Umar Bankaura


Tsohon ɗan wasan kwaikwayon nan Alhaji Umar Yahaya Malumfashi wanda aka fi sani da Bankaura ya bayyana cewa ya na buƙatar addu’a daga wajen al’ummar Annabi saboda yanayin rashin lafiyar da ya ke ciki, wanda ya kai har an kwantar da shi tsawon lokaci a Pinnacle Special Hospital da ke unguwar Hausawa kusa da Masallacin Murtala a jihar Kano, inda ya ke kwance magashiyan.


Bankaura, wanda a yanzu ake kira Yakubu Kafi Gwamna saboda rol ɗin sa a shirin ‘Kwana Casa’in’ ta gidan talabijin na Arewa24, ya na daga cikin daɗaɗɗun ‘yan wasan kwaikwayo da Arewa ke ji da su, domin ya fara dirama ne tun kafin a kafa masana’antar shirya finafinai ta Kannywood.


Yayin da wakilin mujallar Fim ya ziyarce shi Bankaura ya ce, “Kuma dai ka ga a yadda ka same ni. Kuma ina fatan ku ci gaba da yi mani addu’a; Allah shi ya san yadda zai yi da bayin sa.”


Jarumai dai da dama sukan fuskanci matsala ta rashin lafiya wanda abin mamaki sai ka samu babu wasu abokan sana'ar su dake iya daukar dawainiyar su wajen kula da lafiyar su.


A shekarun da suka gabata hakan ya faru da wasu daga cikin jarumai irin su Moda da Sani Sk wanda ya mutu a shekarar da ta gabata a dalilin tsananin rashin lafiya. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post