Irin Kalubalen Da Matan Da Suka Yi Film Ke Fuskanta Idan Sunyi Aure - Inji Zuwaira Abdussalam


Zuwaira Abdussalam wacce tsohuwar jaruma ce a masana'antar Kannywood a shekarun baya ta bayyana wasu kalubale da matan da suka taba yin film suke fuskanta a gidajen aurensu, wanda har sukan kai ga mutuwar auren su. 


A shekarun baya Zuwaira Abdussalam wacce akafi sani da Zuwaira Juda a shekarun baya ta taka rawar gani a fina-finan Hausa, wanda kuma daga baya aka daina ganin ta a masana'antar gabaki daya. 


Wanda sai a wannan lokutan ne ake ganin ta a wasu fina-finai masu dogon zango na "Dadin Kowa" wanda gidan talabijin na Arewa 24 suke yi. Wanda hakan ya baiwa masu kallo mamaki duba da yadda aka dade ba'a ganin jarumar a cikin fina-finai. Sai dai a wata hira da shafin Mujallar Film suka yi da jarumar, sun tambaye ta Ko menene dalilin da yasa aka dauki tsawon lokaci ba'a ganin ta a cikin fina-finan. Inda ta bayyana musu cewa. 


"Na dauki tsawon lokaci ba'a ganina a fina-finan Hausa duk kuwa a lokacin Ina cikin jaruman da suke sharafi. Aure da na yi yasa aka daina ganina, duk da ba kowa yasan na yi aure ba. 


"Amma a yanzu aurena ya mutu, mun rabu dake mijina domin shi aure yana da rai wani lokacin zai iya mutuwa idan kwanan sa ya kare."


Zuwaira ta bayyana matsalar da 'yan film mata suke samu idan sun yi aure, domin sau da yawa mukan samun matsaloli daga wajen dangin miji. Duk da muna zaman aure amma su dangin miji suna yimana kallon 'yan film, basa kallon mu a matsayin matan aure. 


Wasu suna kallon yan film a matsayin marasa tarbiyya kuma karuwai kodai su yi aure haka wasu mutanen ke kallon su wanda ku ma hakan babbar matsala ce fake iya jawo aure ya lalace, cewar Zuwaira. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post