Barnar Da Masu Yabon Annabi Suke Yi A Wakokin Su Yafi Na 'Yan Kannywood Muni - Inji Maryam Fantimoti


Fitacciyar mawakiya Maryam Saleh da akafi kira da Maryam Fantimoti ta bayyana irin baranar da mawakan yabon Annabi (SAW) ke yi wacce tafi na yan film muni. 


A wannan zamanin mata sunfi shiga harkar yabon Annabi (SAW) fiye da harkar film wanda kuma yawancin masu waken barna kawai suke yi a cikin Wakokin su. 


Fantimoti ta bayyana hakan ne a wata hira da  shafin Mujallar Film yai da ita a makon da ya gabata. Inda ta bayyana takaicin ta akan baranar da mawakan yabon Annabi suke yi a wakokin su wanda yafi muni idan aka kwatanta da na 'yan film. 


Fantimoti dai ta kasance a bangare biyu na yabon Annabi (SAW) da kuma wakokin fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood. Ta bayyana rashin tsari ga wasu da suke yabon Annabi. 


Ta ce: “A yanzu mutanen da su ke shiga harkokin wake-wake sha’awa ce; idan mace ta kalli wata a kan mumbari ta na waka, kawai sai sha’awa ta fizgo ta, kawai ta shiga, ba kamar a baya ba da yin wakar baiwa ce ta ke sa mutum ya shiga.


“Mu Allah ne ya ba mu baiwar wakar; a jikin mu ta ke. To a yanzu a taro kawai ka tarar ana waka wai kai ma daga nan ka zama Mawakin Annabi!


“To abin da aka rasa a wajen su masu shiga harkokin wake a yanzu ba su san waka ta na da matakai da dokoki ba, musamman begen Annabi. Sai dai su da yake ba su sani ba kuma sha’awa ce ta kawo su, sai ka ga wata ma wakar kawar ta za ta hau ko ba da izinin ta ba, idan an yi mata magana ta ce ai ita ta ba ta izini. 


“Mu a baya ba haka mu ke yi ba; sai mutum ya ba ka izini za ka zama halifan sa ko idan mutum ya mutu a yi taro a nada halifan sa. Amma a yanzu ka na da rai sai ka ga halifofin ka sun kai goma ko sama da haka.


Ana taba su sai su ce ai halifan wane ne – tun mawakin bai mutu ba, wanda hakan ba daidai bane kuskure ne. 


“Ni kai na da na ke yin magana da kai, sai na ji an bugo mini waya an ce, ‘Ai halifiyar ki ce’. Sai na ce, ‘Ni ba ni da halifa, don ni ban taba yin nadi ba’.


“To, irin abubuwan da su ke faruwa a yanzu kenan. Sai ka ga  mutum ya na da halifofin da bai san yawan su ba.


“Don haka abubuwan da su ke cikin hallara ta yabon Annabi wallahi ba a yin su a cikin wakokin fim na nanaye, saboda kowa ya kwana ya tashi ya san ni Maryam Saleh Fantimoti ina cikin harkar wakar nanaye, kuma ina cikin harkar yabon Annabi. 


“To abin da ya ke cikin hallara ta yabon Annabi ba ya cikin harkar fim ta nanaye, saboda a nanaye babu yadda za a yi mutum ya ɗauki waƙar ka ya yi amfani da ita ba tare da ka ɗaure shi ba, amma a yabon Annabi sai ka je cikin taro za ka yi waƙar ka sai kawai ka ji wata ta hau ta na yi, ka na yin magana sai a ce ai Annabi ne. 


To babu yadda za ka yi. To ka ga a wajen babu kare hakkin mallaka. Idan ka yi wakar, mutane goma sai su dauka su yi amfani da ita kuma ba ka da ikon ka yi magana, sai a ce Annabi ne.”


Fantimoti ta yi kira ga matan aure masu shigowa harkokin waƙen yabon Annabi da su dinga neman izinin mazajen su  haka nan su ma ‘yan mata su dinga neman izinin iyayen su, “domin ana samun matsaloli irin wadannan sosai a wannan harkar ta yabon Annabi.”


A karshe tayi kira da mahukunta da suke dinga daukar hukunci akan irin mutanen da suke dakarun Wakokin wasu suna yin-yang amfani dasu ba tare da izinin su ba. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post