Ma zauna na cikin zullumi tun bayan da aka samu kwarangwal din wani mutum a cikin dakinsa, bayan shekaru hudu da rasuwar sa a garin Apete dake birnin Ibadan na jihar Oyo.
Ana tunanin cewa kwarangwal din gawar (wanda ba a bayyana ba) An samu rahoton tane daga makwabta shekaru hudu da suka wuce ayayin da yake zuwa daga Ibadan zuwa Port Harcourt, a garin River inda anan yake zaune a wannan lokacin.
Har a lokacin hada wannan rahoton ba a samu wani bayani game da abunda ya haddasa wannan kwarangwal din gawar ba.
Ma zauna unguwar sun shaida wa manema labarai cewa, babu wani dan unguwar da ya San da faruwar lamarin har sai a wannan satin, a lokacin da jama'a suka yanke shawarar shiga gidan domin cire ganyayyaki da ciyayin da suka yi yawa har sun fara haddasa macizai a layin.
An tara mutanen da akayi ciniki dasu za su yi aikin cire ciyayin, inda suka haura ta katanga tun daga gate din gidan kulle yake.
Bayan sun haurane suka tarar da motar maigidan tana nan har ganyayyaki da ciyayi sun lullubeta.
A cewar wadanda suka gani da ido, Kamar Yadda jaridar ALFIJIR HAUSA ta rawaito; bayan anyi kokarin cire ganyayyakin ne aka leka ta taga inda suka hangi kwarangwal din mutum kwance bisa gado rike da waya a hannunsa.
Jami'an yan sanda na garin garin Ibadan suna cigaba da bencike akan lamarin domin gano mutumin da kuma danginsa.