Gwamnatin Katsina Ta Hana Siyar da Tabar ‘Shisha’ da sauran Abubuwan kayan maye



Gwamnatin Jihar katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ya sanya hannu a wata sabuwar doka a ranar 5 ga watan Satumba, wacce ta hada da hana yin ta'ammali da amfani da shisha da sauran kayan maye da ba na al’ada ba.


Gwamnatin jihar Katsina ta sanya dokar hana shan shisha da sauran abubuwan da suka saba da addini da al'adu a fadin jihar nan take.


A wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a a Katsina, Daraktan yada labarai na jihar, Buhari Mamman-Daura, ya bayyana haramcin.


Ya ce dokar mai lamba 2022 wacce Gwamna Aminu Masari ya sanya wa hannu a ranar 5 ga watan Satumba, ta hada da hana amfani da shisha da sauran abubuwan sa maye.


A cewar Daraktan, “Wannan ya yi daidai da ikon da aka ba shi na tanadin sashe na 5 karamin sashe na 2 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999, kamar yadda aka gyara.


"Tare da wannan ci gaban, an hana sayar da, shaka ko mu'amala da duk wani abu da ba na magani ba musamman shisha a duk fadin jihar." 


Ya yi ikirarin cewa gwamnati ta yanke wannan shawarar ne bisa la’akari da yadda jihar ke kara tabarbarewar sha’anin matasa.


A cewar sa, duk wanda aka samu da saba wa wannan umarni, zai fuskanci hukunci a karkashin sashi na 114 na dokar Penal Code na jihar Katsina 2021.


A cewar ƙwararrun likitoci, shan shisha yana da haɗarin lafiya daidai da shan sigari kuma yana iya haifar da matsalolin zuciya kamar angina, raunin zuciya, bugun zuciya, ko bugun jini.


Dangane da abun ciki na nicotine, shisha ya kusan kamanta da sigari. Don haka haramunne yin amfani da shisha da duk nau'in ta. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post