Wani mutum ya kashe mahaifinsa dan shekara 90 a jihar Kwara domin samun damar shiga asusun ajiyarsa na bankiRundunar ‘yan sanda a jihar Kwara ta kama wani matashi dan shekara 23 mai suna Ibrahim Hassan da laifin kashe mahaifinsa Sabi Ibrahim dan shekara 90 a unguwar Ajibesin a kan hanyar Okolowo Ilorin domin ya samu damar shiga asusun ajiyarsa na banki. 


“A binciken da ake yi, wanda ake zargin ya amsa cewa ya yi wa mahaifinsa allurar paracetamol da aka hada da wasu abubuwa, bayan da aka yi masa alluran jikinsa ya yi rauni, kuma ya yi kasala, bayan da aka yi masa allurar, ya yi hakan ne bayan ya fito daga banki inda ya kai mahaifinsa ya sabunta tare da karbar katin ATM dinsa. 


Ya dauki uban a kan babur da ya aro ya kai mahaifinsa wani gini da ba a kammala ba ya shake mahaifinsa har lahira, ya tona wani kabari mara zurfi inda ya binne mahaifin nasa bayan ya kwace masa katin ATM da suka je banki ya karba. .'' Ajayi yace


Kakakin ‘yan sandan ya bayyana cewa wanda ake zargin ya tsere zuwa jihar Kaduna ya fara cire kudaden daga asusun mahaifinsa da ya rasu.


Ya ciro jimillar kudi N59,000. Ya kara da cewa dalilin kashe mahaifin nasa shine don ya kwace masa katin ATM tun da ya riga ya san pin din. Ya kuma sayar da babur din da ya ari ya zarce zuwa jihar Kaduna inda a karshe aka kama shi.


An gano katin ATM da babur din da aka sace. Nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu.” Inji Ajayi. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post