AL'AJABI: Wata Mata Ta Haifi 'Ya'ya 9 A Rana Daya Dukkan Su Cikin Koshin Lafiya


Matar mai suna Halima Cisse mai shekaru 25 yar asalin kasar Mali ta haife jarirai tara a rana guda wanda lamarin ya firgita likitoci da masu karbar haihuwar ta. 


Gwamnatin kasar Mali itace ta dauki nauyin Halima inda aka tura ta kasar Maroko domin kulawa daga wajen kwararrun likitoci wanda mijinta ya nuna farin cikinsa a wata tattaunawa da yai da BBC. 


Yace matarsa ta haifi yara tara maza hudu mata 5, kuma dukkan su suna cikin koshin lafiya, a cewar sa. Sannan ya mika godiyarsa ga al'umma daga sassan duniya da suka taya shi murna da kyautar da Allah ya basu. 


Rabon da a samu wata mace da ta haifi jarirai da yawa tun a shekarar 2009 inda wata 'yar kasar Amurka ta haifi jarirai takwas, wanda hakan yasa ta karbi kambun duniya na wacce ta haife jarirai da yawa cikin koshin lafiya. 


A shekarun baya ma dai an samu matan da suka haife jariri takwas a lokaci daya, sai dai ana samun wasu suna zuwa babu rai wasu kuwa babu koshin lafiya. 


Ko a shekarar 1971 a kasar Australia an samu wata mata da ta haife yara takwas, sai wata mata a Malesiya da ta haifi ’yan takwas a 1999, amma babu daya daga cikin jariran da ya rayu bayan kwanaki da haihuwarsu.


Nadya Suleman, ita ce ke rike da kambun Tarihi na Duniya wajen haihuwar yara da yawa lokaci guda, yanzu haka yaran sun girma inda suka kai shekara 12 a duniya. Ministar Lafiya ta Mali, Fanta Siby ta taya ayarin likitoci a Mali da Maroko murnar yadda suka yi hidima har matar ta sauka lafiya.


Nauyin jariran ya kai tsakanin giram 500 zuwa kilo daya, kuma ya ce za a ajiye su a cikin kwalbar kula da jarirai na tsawon wata biyu zuwa uku. Juna biyun Misis Cissé ya zama abin tsegumi a Mali duk da cewa gwajin da aka yi mata a farko-farko ya nuna jarirai bakwai take dauke da su, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya bayyana.


A cewar Farfesa Alaoui, Misis Cissé na dauke da juna biyu na mako 25 lokacin da aka kwantar da ita a asibitinsu kuma likitocinsu sun yi nasarar tsawaita wa’adin cikin zuwa mako 30.


Mijinta Kader Arby, ya ce “Allah ne Ya ba mu wadannan yara, Shi ne Ya san me zai same su, ban damu da abin da zai faru ba, idan Ubangiji Ya yi ikonSa, akwai dalili,” ya shaida wa BBC Afrikue.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post