Sirrin Amfani Da Man Kwakwa Don Rage Tumbi Da Magance Nankarwa


A cikin wannan rubutun za kuji muhimman amfanin da man Kwakwa ke yi wajen yin maganin girman tumbi da nankarwa wanda a turance ake kira da ‘Stretch mark’. 


Wannan matsalolin dai suna damun mata sosai shiyasa muka yi bincike muka kawo muku wani sirri na man kwakwa da za ku iya amfani dashi wajen magance wannan matsalolin da muka ambata. 


A kan samar da danyen man kwakwa ba tare da kona wani abu daga amfaninshi ba. Ba shi da wahalar hadawa, ba a bukatar yin amfani da wuta, kamar yadda na fada a baya.

 

Da farko, uwargida za ta samu kwakwa daidai bukata, sai ta cire bawonsa, ta yayyanka su kanana, sannan ta markade sosai. Bayan kin markade, sai ki tace ruwan, ki zuba a roba, sannan ki ajiye shi a wuri mai iska, ki bar shi ya kwana.


Da safe za ki ga mai ya taso a sama, ki sa cokali, ki yade man, ruwan ne kadai zai rage a kasa. Za ki gan shi kamar man shanu, in kuma kina bukata, kafin ki yade man, sai ki saka shi cikin firji don ya yi kankara. Hakan ya fi dadin yadewa, za ki gan shi kamar man kade. Masana sun tabbatar cewa ya fi dafaffen man kwakwan tasiri.


An nuna cewa za a iya shan shi haka nan domin rage tumbi. Baya ga wannan, za a iya amfani da shi wajen magance Amosanin kai, wato ‘Dandruff,’ don haka za a iya amfani da shi a matsayin sinadarin wanke kai (Shampoo). Ko kuma a hada shi da man kitso da man shafawa domin gyaran jiki matuka.


Ta bangaren warkar da nankarwa kuwa, babu kamar man kwakwa. Da zaran kika fara amfani da shi wajen shafawa a jikinki, tabbas za ki ga nankarwa ta fara ba cewa daga jikin ki. 


Don haka a takaice kwakwa da manta suna da matukar amfani ga mace, bayan wadannan da muka lissafa. Ruwan na magance wasu cututtukan jiki, musamman masu cututtuka a mafitsara, wanda ake kira a Turance ;Urinary infections.’


Allah ya ba mu sa’a, Allah ya taimake mu, da fatan za a wuni lafiya, kuma a rika kula da yara yadda ya kamata.


Man kwakwa ya na da amfani wajen inganta lafiyar fata, gashi, rage nauyin jiki, taimakawa wajen tace abincin jikin mutum da bayar da kariya ga wasu cututtuka da mutum ka iya kamuwa da su. Kiwon lafiya: Amfanin man kwakwa guda 7


1. Kariya ga cututtuka;

Man kwakwa yana bayar da garkuwa ga lafiyar jikin mutum sanadiyar sinadarai na lauric acid, capric acid da caprylic acid. Wadannan sinadai suna inganta kariya na kananan kwayoyin cututtuka irin su kuraje, cutar sanyi da cutar HIV mai karya garkuwar jikin dan Adam.  


2. Gyaran gashi;

Man kwakwa yana bunkasa yalwar gashi kuma ya kawatar da shi wajen kyalli.Yana kuma bayar da kariya ta amosani da rashin karyewar gashi.


3. Lafiyar Hakori;

Akwai sinadarin calcium a cikin man kwakwa wanda yake inganta karfin hakori kuma yake bayar da kariya wajen cututtuka na hakori da kara mu su haske su zama farare tar.


Wannan sune kadan daga cikin amfanin da man kwakwa ke yi ga jikin dan adam musamman mata. Da fatan za'a bada muhimmanci sosai wajen yin amfani da man kwakwa.  


4. Rage nauyin jiki;

Da yawan mutane su na kukan jikin su ya mu su nauyi saboda maiko da yawan teba a jikin su, man kwakwa wanda shima maiko ne amma ya na inganta narkewar duk wani daskararren maiko dake jikin mutum wajen assasasa lafiyar kayan cikin mutum. 


5. Gyara fatar jiki;

Ana amfani da man kwakwa wajen man shafawa a jiki wanda yana da matukar fa'ida ga ma su busashshiyar fata da waskane. Man kwakwa yana kara laushin fata da yadda yake warware tamushewa irin ta tsufa a jikin fata kuma yana fa'idantuwa ga ma su ciwon kyazbi.


6. Tace amfanin abinci;

Akwai ma su fama da ciwon ciki wanda rashin saure tace abinci da su ka ci ke janyo musu, binciken masana kiwon lafiya ya bayyana ingancin man kwakwa wajen inganta wannan matsala ta rashin tace amfani abinci da wuri a cikin mutum.


7.Ciwon Zuciya;

Akwai sindarin lauric acid a cikin man kwakwa wanda ya ke taimakawa wajen rage tasirin hauhawar jini da da rage daskararren maiko wadanda daman su ne ma su assasa ciwon zuciya. Yana kuma fa'idantuwa wajen al'adar mata.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post