Mansurah Isah Ta Gurfanar Da Wasu Matasa A Kotu Kan Ɓata Sunan 'Yarta Imam Sani Danja


Mansurah Isah ta kai karar wasu matasa a gaban kotun majistare dake Kano wanda alkalin kotun ya aike dasu gidan yari har zuwa ranar da za'a cigaba da zaman shariar. 


Mansurah ta bayyana mana cewa ta kai karar matasan gaban kotu kan zargin su da yin amfani da sunan 'yarta Khadijatu Sani Danja wacce ake kira da Iman suna aikata abubuwan da basu dace ba a kafar soshiyal midiya. 


Tun da fari sai da tsohuwar jarumar ta kai korafi ga ofishin Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da ke Kano inda ta ce wasu na amfani da sunan ‘yar ta a Facebook, Instagram da TikTok su na yada labarai da hotunan da ba su dace ba. 


Duk da nufin Iman din ce ta ke da wadannan shafuka, alhalin ita sam ba ta hawa gizo-gizo da sunan ta, kuma babu wani shafi da ta ke yin amfani da shi na kashin kan ta.


Wanda hakan yasa hukumar tsaron suka yi bincike har su ka kamo matasan guda biyu waɗanda ake zargi da laifin. Wanda kuma daga bisani aka gurfanar dasu a gaban kotu. 


A zaman da aka yi, alkalin ya tura matasan zaman gidan yari na kwana uku domin cigaba da binkice akan lamarin tare da kamo karin wani mutum daya da ake zargin su. 


Munyi kokarin jin ta bakin wadanda ake zargi da aikata laifin sai dai ba mu samu damar yin magana dasu ba. Amma mun samu mun tattauna da Mansurah inda ta bayyana mana cewa ana yin amfani da sunanta wajen turawa mutane sakonni na abubuwan da basu dace ba. 


Mu kuma tunda ba mune muke yi ba ba za mu jure hakan ba, a matsayin mu na iyaye ba za mu jure muga ana yiwa 'ya'yan mu sharri ba, hakan yasa muka dauki matakin zuwa kotu domin abi mana hakkin mu.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post