Gwamnatin Jihar Kano Na Neman Ado Gwanja Ruwa A Jallo Akan Wakar Asosa


Biyo bayan fitar da sabuwar wakar da Ado Gwanja yai ta Asosa mahukunta sun fara neman sa ruwa a jallo. Sai dai an bayyana cewa Ado Gwanja baya garin Kano. 


Hukumar tace finafinai da dab’i ta jihar Kano, karkashin jagorancin Ismaila Na’abba Afakallah, tace zata hukunta mawakin Hausa Ado Gwanja matukar dai an same shi da abinda ake korafi akansa.


Cikin wani jawabi ga manema labarai, Afakallah yace duk daukakar mutum zasu hukunta shi matukar dai ya aikata laifin da yaci karo da dokokin hukumar, ba sani ba sabo.


Tuni dai lauyan nan Barista Sulaiman Gandu tare da wasu lauyoyi suka shirya tsaf domin garzayawa gaban kotun don kalubalantar Gwanja akan sabuwar wakarsa mai taken “Chas” wacce suke ganin anyi amfani da kalaman rashin mutuntaka da fitsara a cikinta.


To amma kuma a nasa bangaren, Gwanja yace wakar tuni ya siyar da ita, saboda haka yanzu bashi da iko akanta, kuma ko bai siyar ba, ba lallai ya karbi bukatar da aka zo masa da ita ba, domin ba’a bashi sana’a ba, bazai yiwu kuma a hana shi tasa sana’ar ba.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post