Yanzu-yanzu Aisha Najamu Tayi Kakkausar Suka Akan 'Yan Hisbah Game Da Wakar Ado Gwanja Ta Asosa


Biyo bayan Cece-Kuce da ake ta yi akan sabuwar wakar da Mawaki Ado Gwanja yai mai suna "Asosa" wacce ta dauki hankalin jama'a musamman mata yasa mahukunta suka dakatar da mawakin fitar da wakar.


A baya-bayan nan wani Lauya a jihar Kano yai kira da hukumar Hisbah da su yi gaggawar kamo Ado Gwanja domin dakatar dashi da fitar da sabuwar wakar sa ta "Asosa", wanda yace idan ba su kamo shi ba zai gurfanar dasu a gaban kotu.


Sai dai daga bisani Ado Gwanja ya mayar da martani ga Lauya inda yace babu wanda ya isa ya hanashi fitar da wakar sa ba.


Itama jaruma Aisha Najamu wacce aka fi sani da Aisha Izzar so ta fito ta bayyana cewa ba ta ga dalilin da zai sa a hana Ado Gwanja fitar da wakar sa ta Asosa ba. 


Kalli cikakken bidiyon da tai magana 👇👇Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post