Yanzu-Yanzu: Wasu Daga Cikin Fasinjojin Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Sun Kubuta Daga Hannun 'Yan Bindiga


Rahotanni dake fitowa daga Najeriya na tabbatar da cewa wasu mutum uku daga cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, sun kubuta sa’o’i 24 bayan da ‘yan ta’addan da suka sace su, sun fitar da wani hoton bidiyo mai tayar da hankali suna azabtar da su.


Jaridar Aminiya ta rawaito cewa an kubutar da mutane 3 wanda ya hada mace daya da maza biyu wanda suka sake haduwa da iyalan su da ‘yan uwansu.


Ba a bayyana ko an biya kudin fansa kafin a sake su ba. Sai dai wani mawallafi mazaunin Kaduna, Tukur Mamu ya tabbatar da jaridar Aminiya sakin fasinjojin. 


“Eh uku daga cikin wadanda abun ya rutsa da su sun kubuta, an saki mace daya da maza biyu. Amma ka sani ban shiga tsakani don sakinsu ba.” A cewarsa.


Idan dai za a iya tunawa Mamu ya fice daga shiga tsakani don yin sulhu sakamakon barazana da ake yi wa rayuwarsa.


A ranar Lahadi ne ‘yan ta’addan fa suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, suka saki wani bidiyo da ya nuna yadda suke azabtar da fasinjojin.


Sai dai bidiyon ya yamutsa hazo, inda mutane da dama ke ganin gwamnatin tarayya ta gaza yin wani abu don ceto fasinjojin.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post