Wata Matar Aure Ta Kashe Mijinta Saboda Zai Kara Aure


Rahotanni ya tabbatar da cewa matar ta hallaka mijinta ne ta hanyar zuba masa guba a cikin abinci kawai don yana shirin Kara aure. 


Matar dai da mijinta sun shafe shekaru 12 da yin aure amma rana daya ta yi masa wannan aika-aikar duk saboda zai yi mata kishiya. 


Lamarin dai ya faru ne a ranar Lahadi a unguwar Apo dake Masaka a Jihar Nasarawa. 


Jaridar Aminiya ta rawaito cewa ma'auratan suna samun sabani akai-akai tun bayan da mijin ya bayyana cewa zai kara aure. 


Rahotan yace a kwanaki matar ta taba kwashe kayan ta daga gidan mijinta na tsawon lokaci wanda daga baya ya auri wata matar. 


Wani kanin marigayin ya ce, “Dan uwana na yawan yin korafi kan matar tasa; wani lokaci ko abinci ba ta ba shi.


“Domin a samu zaman lafiya, sai ya nemi mu yi mata magana, mutane suka zo aka yi mata magana, amma ba ta ce komai ba.


“Ranar Lahadi sai muka ji hayaniya a gidan, sai muka garzaya muka shiga, ko da muka je sai muka samu ta riga ta yi mishi wanka da gubar asid, har jikinsa na zagwanyewa.


“Mun kai shi asibiti amma suka ki karbar shi, shi ne muka kai shi wani wurin, daga baya ya rasu ranar Litinin da safe.”


Wani dan uwan mamacin ya ce sun riga an yi mishi sutura bisa tsarin addinin Musulunci kuma sun shiga neman matar.


Har aka kammala hada wannan rahoto ba a samu jin ta bakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Nasarawa ba.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post