'Yan Bindiga Sun Kashe Sojojin Tsaron Tawagar Shugaban Kasa A AbujaWani hafsan soja mai mukamin Kyaftin tare da kananan sojoji biyu daga Rundunar da ke Tsaron Shugaban Kasa sun kwanta dama a harin ’yan bindiga a yankin Babban Birnin Tarayya, Abuja.


Sojojin daga Rundunar da ake kira ‘7 Brigade of Guard Nigerian Army’ sun gamu da ajalinsu ne a harin kwanton bauna da ’yan bindigar suka yi musu a Abuja.


Hakan na zuwa ne kimanin awa 24 bayan ’yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun yi barazanar sace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da wasu manyan jami’an gwamnatinsa.


Majiyarmu ta soji ta shaida mana a ranar Litinin cewa lamarin ya rutsa da sojojin ne bayan sun samu kiran dauki daga Makaran Koyan Aikin Lauya da ke Bwari a Abuja.


A ranar Lahadi ce suka samu kiran bayan hukumar makarantar ta samu wasikar barazanar hari daga ’yan bindiga.


Majiyar ta ce, “Bayan samun wasikar barazanar ce hukumar makarantar ta sanar da hukumomin sojin Rundunar 7 Guards Brigade.


“An tura Kyaftin din tare da wasu sojoji zuwa makarantar domin gudanar binciken sharar fage, inda suka gana da hukumar makarantar kan matakan da za a dauka domin tabbatar da tsaron dalibai da malamai da kayan aiki.


“Abin takaci a hanyarsu ta komawa ce aka yi musu kwanton bauna aka kashe Kyaftin din da kananan sojoji biyu”.


Ta kara da cewa sauran sojojin da ke cikin ayarin kuma sun sha da kyar a harin ’yan ta’addar.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post