Boko Haram Na Shirye-Shiryen Kai Hari A Babban Masallacin Kasa Na Abuja


Mayakan Boko Haram da ‘yan bindiga na shirin kaddamar da farmaki kan babban Masallaci na kasa da kuma Makarantar Horas da Lauyoyi da ke babban birnin Abuja kamar yadda Jaridar Daily Nigerian ta rawaito.


Jaridar ta ce, wata sahihiyar majiya ta shaida mata cewa, ‘yan ta’addan karkashin jagorancin Kachalla Ali Kawaje da Kachalla Dansadi na kitsa yadda za su sace malamai da dalibai daga Makarantar ta Horas da Lauyoyi da ke Bwari.


Tuni ‘yan ta’adda suka nazarci tsare-tsaren tsaron da ke Makarantar domin sanin yadda za su kaddamar da farmakin da miyagun makamai  da suka hada da rokoki kamar yadda Daily Nigerian ta ambato.


Har ila yau, ‘yan ta’addan na shiirn dasa bama-bamai a kusa da harabobin Masallatai da Coci-coci da sauran wuraren al’umma.


Majiyar ta ce, babban Masallaci na kasa, shi ke kan gaba a shirinsu na kaddamar da farmakin.


Wannan na zuwa ne bayan Ma’aikatar Ilimi ta Kasar ta bada umarnin rufe makarantun hadaka na sakandaren gwamnatin tarayya da ke Abuja saboda fargabar fuskantar hari daga ‘yan ta’addar.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post